2 Corinthians 2

1Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba. 2Gama in na sa ku baƙin ciki, wa ya rage yǎ faranta mini zuciya, in ba ku waɗanda na sa baƙin cikin ba? 3Na rubuta yadda na yi ne saboda saʼad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka. 4Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, aʼa, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.

Gafara don Mai Zunubi

5In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne. 6Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka. 7Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma taʼazantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yǎ sha kansa. 8Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku. 9Abin da ya sa na rubuta muku shi ne don in ga ko za ku jimre da gwajin nan, kuna kuma yin biyayya ta kowace hanya. 10In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa-in har ma da abin gafartawa-saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi, 11don kada Shaiɗan yǎ rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.

Masu Hidimar Sabon Alkawari

12To, saʼad da na tafi Toruwas don in yi waʼazin bisharar Kiristi, ko da yake na tarar cewa Ubangiji ya buɗe mini ƙofa, 13duk da haka, ban sami salama a zuciyata ba domin ban sami ɗanʼuwana Titus a can ba. Sai na yi bankwana da su na wuce zuwa Makidoniya.

14Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a koʼina. 15Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka. 16Ga wani, mu wārin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yǎ yi irin wannan aikin? 17Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.

Copyright information for HauSRK